Hare haren birnin Bagadaza ya kashe mutane masu yawa | Labarai | DW | 02.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hare haren birnin Bagadaza ya kashe mutane masu yawa

Boma bomai sun tarwatse a cikin motoci daban daban guda ukua tsakiyar birnin Bagadaza,wanda ya kashe mutane 40 nan take,bayan kimanin 80 da suka raunana.Sanarwar yansanda na nuni dacewa zaa iya samun karuwan adadin wadanda suka rasa rayukansu,daga hare haren na yau.Kazalika,a yau din ne kuma wasu mutane 18 suka gamu da ajalinsu,alokacinda wata babbar mota dake tafiya da gudu,tabi kann mutane dake tsaye a tashar motocin bus,a unguwar Al-Wahada,mai tazarar km 35 kudancin Bagadaza.Matukin motar daya nemi gudu,kafin a cafke shi yace birkinsa ne ya samu matsala.A wani yankin na birnin na Bagadazan kuwa ,wasu mutane tara aka kashe a yau din,alokacinda wasu sojin sakai suka kaddamar da hare haren boma bomai da harbin bindigogi.