Hare-haren bama-bamai a Pakistan. | Labarai | DW | 19.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hare-haren bama-bamai a Pakistan.

Hausawa kance wai maƙwabcin mai kanwa bai rasa balbaɗi, kamar yadda Afghanistan ke fama da tashe –tashen hankula, maƙwabciyar ta Pakistan, ita ta tsunduma cikin wannan hali, tun bayan murƙushe tarzomar yan takifen jan masalacin Islamad, a makon da ya gabata.

Da sanhin sahiyar yau, wasu yan takife sun tarwatsa bama-bamai, a tsakiyar kasuwar Hub Chowk, da ke kudancin ƙasar inda a nan take mutane 10 su ka kwanta dama.

Wannan shine hari na farko, da ya rutsa da yankin Baluchistan da ke kudancin Pakistan.

Shugaban rundunar yan sandar yankin, ya ce a halin yanzu sun fara bincike, domin gano ko wannan hari na da nasaba da hare-haren ta´dancin da su ɓarke a Pakistan a ƙarshen makon da ya wuce, wanda kuma su ka yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 70.

Har ya zuwa yanzu ,babu ƙungiyar da ta fito ƙarara ta ɗauki alhakin kai wannan hari, wanda bisa dukkan alamu a ka seta shi, a kan wata tawagar yan ƙasar Sin, dake aikin haƙo Gaz a yanki baloutchistan.