1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hare-haren bama-bamai a Damaturu

November 5, 2011

Mutane da dama sunrasa rayuka wasu kuma sun ji raunuka a hare-haren bama-baman da suka rutsa da Damaturu babban birnin jihar Yobe a Najeriya

https://p.dw.com/p/135fr
Hoto: AP

Aƙalla bama-bamai biyar suka tarwatse ranar Juma´a yankin arewa maso gabacin Najeriya abinda ya saka ruɗami ga mazauna wannan yanki.

A Damaturu babban birnin jihar Yobe, bam ɗin ta fashe kusa da wani ofishin `yan sanda.Cemma kamin nan, saida wasu tagwayen bama-bamai suka fashe a birnin Maiduguri inda mutame da dama suka ji raunuka.

Wanda suka ganewa idonsu yadda hare-haren sunce 'yan ƙunar bakin waken aƙalla uku suka mutu.

Jami´an tsaro na zargin ƙungiyar Boko Haram da kitsa wannan hare-hare.

A halin da ake ciki mazauna Damaturu sun shiga wani na ruɗami, duk da cewar gwamnati ta yi bayyana aniyar zaƙulo wanda ke da alhakin kai wannan hare-hare.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Usman Shehu Usman