Hare-Haren Bam a Najeriya | Labarai | DW | 01.10.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hare-Haren Bam a Najeriya

Mutum 8 sun rasa rayukkan su a dandalin gudanar da bukukuwan cika shekaru 50 a Najeriya

default

Shugaba Goodluck Jonathan

A Najeriya yayin da ake gudanar da bukuwan cikar ƙasar shekaru 50 da samun 'yancin kai, rahotanni sun ce an sami tashin wasu jerin bamabamai uku a kusa da dandalin da shugaban kasar Goodluck Jonathan ya gabatar da jawabi. An rawaito cewa biyu daga cikin bamabaman sun tashi ne a wasu ƙananan motoci guda biyu, yayin da ɗaya bomb din ya fashe a daidai lokacin da zaa fara parati a dandalin eagle square. Rahotannin farko sun ce aƙalla mutane 8 suka rasa rayukan su, ciki har da ɗan sanda ɗaya, bayan da wasu da dama suka sami raunuka.

Harin ya auku ne, bayan barazanar da wata kungiyar yan ta kife ta yi na cewa babu wani cigaba na a zo a gani a tsawon shekaru 50 ɗin, da ma zai kai ga waɗannan bukukuwa.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu

Edita: Umaru Aliyu