Hare haren bam a Iraki | Labarai | DW | 19.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hare haren bam a Iraki

A kasar Iraqi bama bamai shida da aka dasa cikin motoci sun halaka mutane 19 cikin birnin Bagadaza yayinda firaministan kasar ya bukaci Amurka data bada karin makamai ga dakarun kasar.

Daya yake maida martani cikin hira da akayi da shi a wani gidan rediyo na Amurka,shugaba Bush yace sabbin dabaru da ya sanar makon daya gabata game da Iraqin,ya tsara su ne tare da nufin taimakawa gwamnatin Iraqin ta samu makaman.

A halinda ake ciki kuma maaikatar tsaro ta Iraqi tace abinda take bukata a wannan yaki ya kai euro biliyan 6 da rabi.