1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hare-haren ƙunar baƙin wake a Irak

A cigaba da hare haren ƙunar baƙin wake a ƙasar Irak, mutane 8 fara hulla, da yan sanda 6 sun rasa rayuka yau da assuba, kussa da birnin Bagadaza, sannan an gano wasu gawwaki 18.

A ɗaya wajen ƙungiyar yan jarida ta dunia, ta bayyana sanarwar kashe wasu yan jarida guda 2, a birnin Mossoul.

Daga farkon yaƙin Irak zuwa yanzu, baki ɗaya, yan jarida 70 su ka riga mu gidan gaskiya, a lokacin da su ke gudanar da aiki.