1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hare-haren ƙunar baƙin wake a Algiers

Ƙasashen Faransa da Spain da kuma Italiya sun yi Allah wadai da harin ƙunar baƙin wake da aka kai birnin Algeirs na ƙasar Algeria.Harin a cewar ƙasashen abune daka iya dawo da hannun agogo baya, dangane da yaki da ayyukan ta´addanci da ƙasar keyi. Da ranar yau ne birnin na Algiers ya fuskanci tashin tagwayen bama- bamai. Yawan mutanen da su ka rasu a yanzu haka ya kai 60. Mutane goma daga cikinsu Jami´an diplomasiyya ne na Majalisar Ɗinkin Duniya. Harin ya kuma haifar da jikkatar wasu mutanen da daman gaske.