1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hare-haren ƙunar baƙin wake a Iraƙi

Abdourahamane HassaneMarch 6, 2016

'Yan sandan Iraƙi sun ce mutane 29 ne suka mutu yayin da wasu 47 suka jikkata .Hotuna sun nuna ɓarna da aka haddasa a wurin binciken ababen hawa a Iraki

https://p.dw.com/p/1I8AM
Irak Autobombenanschlag in Bagdad
Hoto: Reuters/K. al-Mousily

Harin ya afku ne bayan da wata motar da aka ɗana wa bam ta yi bindiga ta kuma fashe a wani wurin binciken ababen hawa da ke a Hilla a Kudancin Bagadaza. Hotunan da aka nuna ta hanyoyin intanet na sada zumunta na nuna ɓarna da aka haddasa a wurin binciken ababen hawar a daidai lokacin da motoci suka ja dogayen layuka a wurin.

Kawo yanzu babu wata ƙungiya da ta yi iƙirarin kai harin. Amma ana kyautata zaton cewar Ƙungiyar IS ce ke da alhakin kai harin.