Hare-hare sun kashe rayuka a Najeriya
February 17, 2018Talla
Wasu 'yan kunar bakin wake sun kaddamar da hare-hare a wata kasuwa da ke jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya, inda kimanin mutane 20 suka salwanta wasu sama da hakan kuwa suka jikkata. Hare-haren da suka auku da almurun jiya Juma'a, sun faru ne a garin Konduga kimanin mil 20 daga Maiduguri babban birnin jihar.
Rundunar 'yan sandan Bornon, ta bakin kakakinta Joseph Kwaji, na zargin maharan mata ne. Ta'asar dai na zuwa ne makonni da shari'ar wasu da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne da ke gwagwarmaya da makamai a Najeriyar.