1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hare hare a jihar Yobe

July 1, 2012

Haɗin giwar jami'an rundunar tsaro ta JTF a Tarrayar Najeriya sun kai wani samame akan ƙungiyar Boko Haram a Damaturu

https://p.dw.com/p/15P1u
Hoto: AP

An bada rahoton cewar an kashe mutane guda ukku a cikin wasu hare da jami'an tsaro suka kai a Damaturu hed kwatar jihar Yobe da ke a yanki arewa maso gabacin Tarrayar Najeriya.Masu aiko da rahotanin sun ce da yamanci jiya an ji ƙarar fashewar wasu abubuwa, sailin da dokar hanna fita ta fara aiki a unguwanin da dama na hed kwatar.

A lokacin da wani haɗin gwiwar jami'an rundunar tsaro ta JTF da ke yin sintiri ya gano wasu yan ƙungiyar Boko haram waɗanda suka yi musanyar wuta da su. A cikin watan Yuni da ya wucce ne hukumomin Najeriya suka kafa dokar hana fita a jihar ta Yobe saboda yawan hare haren ta'adancin da ke ƙara tsanata a yanki.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman