Hare hare a Iraki sun halaka daruruwan mutane | Labarai | DW | 15.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hare hare a Iraki sun halaka daruruwan mutane

A kasar Iraqi aklla mutane 200 ne suka rasa rayukansu wasu fiye da 300 kuma suka jikkata a daya daga cikin hare haren bam mafiya muni cikin shekaru 4 na yakin kasar.Rahotanni sunce an kai hare haren ne cikin wasu manyan motoci guda hudu a unguwar yan darkar yazidi kusa da Mosul a arewacin kasar ta Iraqi.Kafofin yada labarai na kasar sunce bama baman cikin motoci biyu sun tashi ne a bayan juna a bakin rukunun gidaje na siba sheikh Khidr.daga bisani kuma aka kaddamar da hari a dai wannan yanki bayan fashewar bama baman.A halinda ake ciki kuma wasu yan bindiga sun sace ministan kula da albarkatun mai na Iraqin haka kuma wasu sojojin Amurka 5 sun halaka bayan helikopta da suke ciki ya fado.Tun farko a ranar talatan kuma wani dan kunar bakin wake ya lalata wata gada a wajen babban birnin kasar Iraqin,inda ya halaka mutane 8 tare kuma da katse hanyar da ta hade birnin Bagadaza da lardunan arewacin kasar.A yau din nan kuma mutane 2 suka rasa rayukansu wasu 7 suka jikkata cikin wani harin a kudancin Bagadaza.