1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

hare-hare a Irak

May 11, 2005

An ci gaba da fama da hare-haren kunar bakin wake a kasar Irak yau laraba da sanyin safiya

https://p.dw.com/p/Bvc3
hare-hare a Tikrit
hare-hare a TikritHoto: AP

Rahotanni na baya-bayan nan sun ce sama da mutane 70 suka mutu sakamakon harin kunar bakin waken na yau laraba, wanda wani bangare ne na hare-haren sare ka noke da kasar ke fama da shi, wanda kuma ya kashe kusan mutane 400 tun bayan da aka nada sabuwar gwamnati a kasar Iraki makonni biyu da suka wuce. A garin Tikrit wata mota ta yi bindiga a tsakanin dimbin ‚yan shi’a, wadanda suka yi cincirindo domin neman aiki. Harin an kai shi ne a kusa da wata tasha ta ‚yan sanda ya kuma halaka mutane 33 sannan ya ji wa wasu 80 rauni. A can garin Hawija dake kusa da Kirkuk mai arzikin mai a arewacin Irak wani dan kunar bakin wake ya kutsa kai a wata cibiyar daukar soja, inda ya cunna bom din dake daure da shi tare da halaka mutane 32 da kuma ji wa wasu 34 rauni. Daya harin kuma an kai shi ne a wani yankin dake kudancin Bagadaza tare da kisan farar hula guda uku. Sannan wasu majiyoyi na ma’aikatar cikin gida kuma suka ce an kai hari kann ‚yan sanda dake sintiri a Bagadaza, inda ‚yan sanda biyu da kuma wani farar hula daya suka halaka. Tun bayan kafa sabuwar majalisar ministocin Irak a ranar 28 ga watan afrilun da ya wuce ake fama da hare-haren sare ka noke a duk fadin kasar. A baya ga haka, masu alhakin hare-haren suna ci gaba da sace mutane domin garkuwa da su. A karshen watan afrilun da ya wuce an tsare wani dan kasar Autralia dake da shekaru 63 da haifuwa, domin tilasta wa gwamnatin kasar ta janye sojojinta daga Irak. A kuma ranar lahadi da ta wuce an kame wani dan kasar Japan mai shekaru 44 da haifuwa, kuma tuni dakarun kungiyar Ansarusunna suka ce su ne ke garkuwa da shi. Dukkan kasashen Australia da Japan dai sun taimaka wa Amurka wajen kai hari kann kasar Irak, kuma sun ce ba zasu janye sojojinsu daga kasar ba. Kuma har ya zuwa halin da muke ciki yanzu ana ci gaba da garkuwa da gwamnan jihar Anbar, inda masu garkuwa da shi suka shimfida sharadin sakin dukkan mayakan Abu Musab Zarqawi dake tsare, kafin su sake shi. A daya bangaren kuma sojojin Amurka sun shiga kai hare-hare a yankin hamadar Qaim, inda aka ce ta nan ne ake satar hanyar shigowa da mayaka na ketare daga Siriya zuwa Irak. Rahotannin da muka samu sun ce sojojin Amurka guda uku aka kashe a karkashin wannan mataki, wanda ya kai adadin sojan Amurka da suka halaka a Iraki zuwa sojoji 14 tun daga ranar asabar da ta wuce.