Hare-hare a Irak | Labarai | DW | 13.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hare-hare a Irak

A ƙasar Iraki tashe –tashen hankulla na daga bazuwa duk da mutuwar shugaban ƙungiyar Alqa´ida Abu Mussab Alzarqawi.

A sahiyar yau, wasu bama bamai 5 su ka tarwatse a tsukin sa´o´i guda 2, a birnin Kirkuk.

Wannan hare-here sun hadasa mutuwar mutane 18 tare da jima wasu da dama.

Ƙungiyar Alqa´ida a kasar ta bayyana nada wani saban jogaran wanda Amurika ta ce, shima kwanikan sa ƙirgagu ne.

A na ta kai wannan hare hare a lokacin da Amurika ke shirya taro, a game da makomar ƙasar.

Daga mahimman batutuwan da shugaba Bush ke tantanawa da muƙaraban sa, da kuma wakilan gwamnati Iraki har da batun zaman sojojin Amurika.

A ci gaba kuma da shari´ar tsofan shugaban ƙasa Saddam Hussain, yau ƙanan sa, wato Barzam al Tikriti, bai halarci ba kotun, bayan sa insa da yayi hjiya da alkali mai sharia´a.