Hare hare a Ceceniya | Labarai | DW | 19.10.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hare hare a Ceceniya

'Yan tawayye sun kai farmaki a ginin majalisar dokokin Ceceniya

default

rahotanin da ke zuwa mana yanzu yanzu nan na cewa wasu yan tawayye sun kai a hare hare a ginin Majalisar Dokoki na kasar Ceceniya.Wanda a sakamakon wannan hari rahoton ya nuna cewa an samu asara rayukan jama'a sannan kuma yan tawayyen sun yi garkuwa da wasu jama'ar.

Kuma kamfanin dilanci labarai na Interfax ya shaida cewa shi kansa shugaban majalisar ya na cikin gidan a sa'ilin wannan hari kuma yazuwa yanzu ba a san abinda ke faruwa ba.

Kuma a halin da ake ciki wasu rahotannin na nuni da cewa sojojin kasar na Ceceniya sun yi nasara karkashe maharan dukaninsu tare da yin belin mutane da suka yi garkuwa da su.

Mawallafi : Abdurahamane Hassane

Edita : Umar Aliyu