1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hare hare a Agadez da Arlit na Nijar

May 23, 2013

Wasu mahara da ba a san ko su wanene ba sun tarwatsa motoci a kofar barikin sojoji da ke Agadez da kuma kanfanin hako ma'adinai na SOMAIR a arewacin Jamhuriyar Nijar.

https://p.dw.com/p/18cRm
Hoto: picture alliance/Ferhat Bouda

Wasu mutane da ake zaton cewar masu kaifin kishin addini ne da aka kora daga Mali sun kai hare-hare a wani barikin sojojin na garin Agadez da kuma a cibiyar kamfanin hakar uranium na SOMAIR da ke a garin Arlit. Rahotannin da muka samu sun nunar da cewar maharan sun tarwatsa wata mota a kofar barikin sojen na AGgadez kafin su kutsa ciki. An ta musayar wata tsakanin maharan da kuma sojojin Jamhuriyar ta Nijar. Yayin da a garin Arlit maharan suka tarwatsa wat mota a kofar kamfanin na SOMAIR.

Da misalin karfe biyar na safiyar wannan alhamis ne aka soma jin karar fashewar wasu
abubuwa da kuma harbe harban bindigogi a garin na Agadez. Sai dai kuma bayanan da wakilin DW ya samu sun nunar da cewar kura ta dan lafa bayan da sojojin gwamnati suka fatattki maharan.

Mawallafi:Gazali Abdou/ Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu