Hare-hare a Afganistan
September 17, 2010Talla
Ƙungiyar mayaƙan taliban a ƙasar Afganistan ta yi awan gaba da wasu mutane guda 19 a ciki hadda ɗan takara guda, a jajibirin zaɓen ´yan majalisun da za a gudanar a ƙasar a gobe asabar idan Allah ya kaimu
Mutanen waɗanda suka haɗa da ´yan siyasa da kuma wasu ma´aikatan hukumar zaɓen an sace su ne a Bad-ghis yankin da ke a arewa maso yammacin ƙasar
Kimanin mutane miliyan goma ne ake sa ran zasu kaɗa ƙuri´a a zaɓen domin zaɓen wakilan ´yan majalisun na jirga 249
Sai dai a halin da ake ciki masu lura da al'amuran yau da gobe na hasashen cewa jama´a ƙalilan ne zasu fito saboda barazanar da ƙungiyar ´yan taliban ɗin ta yi na kai hare hare a runfunan zaɓen
Mawallafi: Abdourahman Hassane Edita: Yahouza Sadissou Madobi