Hare-hare a ƙasar Irak | Labarai | DW | 07.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hare-hare a ƙasar Irak

A ci gaba da yaƙe yaƙe a Irak ,mutane fiye da 10 sun rasa rayuka, a yau talata, a yayin da wasu da dama su ka ji mumuman raunuka, a sakamakon hare hare, barkatai, da yan ƙunar baƙin wake su ka kai a sassa daban daban na ƙasar.

A ɓangaren pirsinoni da ke tsare a gidajen kurkukun Irak, ƙungiyoyin kare haƙƙoƙin bani adama, sun zargi Amurika da ci masu zarafi, da kuma tsare su, babu gaira babu dalili.

A sahiyar yau,ɗaya daga cikin pirsinoni 8500 ,da ke gidan yarin Bucca, a kudancin Irak, ya kwanta dama,sanadiyar ciwon bugun zuciya.

Sannan gidan Talbajan na Aljazira, ya nuna paipen Videon wasu turawa 3, da aka yi garkuwa da su, su na masu kira ga shugabanin ƙasashen yankin Golf, da gwamnatocin ƙasashen su, su ceci rayukan su.