Haramcin zirga zirgar jiragen sama tsakanin Jamus da Yemen | Labarai | DW | 02.11.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Haramcin zirga zirgar jiragen sama tsakanin Jamus da Yemen

Jamus ta haramta jiragen saman ɗaukar fasinja ko kuma na kaya daga Yemen su yada zango a ƙasar

default

Filin jirgin saman Cologne a Jamus

Jamus ta haramta ɗaukacin jiragen sama dake tashi kai tsaye ko kuma ta hanyar yada zango a wasu wurare daga ƙasar Yemen zuwa ƙasar ta Jamus, bayan da hukumomin na Jamus suka gano cewar, wani ƙunshin bam da aka bankaɗo yana kan hanyar sa ta zuwa Amirka daga Yemen ya biyo ta Jamus ne a ranar Jumma'ar da ta gabata.

Hakanan wannan haramcin zai shafi jiragen ɗaukar kaya da na fasinja na mako makon da ke zuwa Jamus bayan yada zango a birnin Roma na ƙasar Italiya. Wani kakakin gwamnatin Jamus a birnin Berlin ya kuma sanar da cewar, hukumomin na Jamus za su fa'ɗaɗa ɗaukar irin wannan matakin ga wasu jiragen ɗaukar kaya da kuma na Fasinja daga wasu ƙasashen. Tun bayan bankaɗo saƙon bam ɗin ne dai ƙasashen Amirka da Birtaniya da kuma Faransa suka ɗauki makamancin waɗannan matakan.

A nata ɓangaren ƙasar Yemen ta mayar da martanin ta ga matakin haramcin da cewar, abin taƙaici ne kuma mai ban mamaki, inda ta kwatanta hakan da cewar, babu basira wajen hukunta jama'a baki ɗaya saboda matsalar yunƙurin aika ƙunshin bam ɗin.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Abdullahi Tanko Bala