Haramcin zirga-zirgan dare a iyakokin Burkina Faso da Mali | Labarai | DW | 09.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Haramcin zirga-zirgan dare a iyakokin Burkina Faso da Mali

Kasar Burkina Faso ta haramta duk wata zirga-zirga ta cikin dare kan ababen hawa a iyakokinta da kasar Mali. Matakin ya fito ne a ranar Laraba daga gwamnan yankin Kanal Hyacinthe Yoda.

Togo Burkina Fasos Präsident Roch Marc Christian Kabore beim AU-Gipfel (picture-alliance/AA/A. Logo)

Shugaban kasar Burkina Faso Roch Marc Christian Kabore

Gwamnan ya ce hanin ya shafi duk wasu masu motoci, ko babura, har ma da masu laulawa ko keke. Kuma yana somawa ne tun daga misalin karfe biyar na yammaci zuwa karfe shida na safe. Sanarwar ta Burkina Faso ta ce wannan hani ya shari yankuna kamar na Baraboule, Nassoumbou, Koutoukou, Deou, Oursy, da kuma Markoye dukanninsu da ke a iyakan kasashen biyu na Burkina Faso da Mali a yankin arewacin kasar ta Burkina Faso.

Kasar ta Burkina Faso dai ta fuskanci hare-hare a 'yan lokuttan baya-bayan nan daga 'yan ta'adda da ke fitowa daga kasar Mali, wanda kuma take ganin yin hakan, shi ne zai iya taimakawa wajen kawo karshen hare-haren da take fuskanta.