1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Haramcin zanga zanga a ƙasar Guinea

Wasu jam'iyun siyasa sun yin brazanar yin zanga zanga a ƙasar Guinea sai dai hukumomin sun hana

default

Shugaban gwamnatin mulkin soja na ƙasar Guinea Sekouba Konate

  Gwamnatin mulkin soja na riƙon ƙwarya a ƙasar Guinea ta haramta wata zanga zanga da yan siyasar ƙasar suka so a yau litinin domin nuna damuwarsu dangane da makuɗin da suka ce an tabka a zagaye na farko na zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a makon jiya.

Na gaba ne  dai a ranar 18 ga wannan wata da muke cikinsa aka shirya za a yi zagaye na biyu na zaɓen, tsakanin tsofon friministan ƙasar Cellou Dalein Diallo wanda ke gaban da yawan ƙuri'u dakuma jagoran yan adawar Alpha Conde.

To amma jam'iyun siyasar da dama da aka zubda tun a zagaye na farko  suna kira da cewa an yi aringizo na ƙuri'u a zaɓen.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane

Edita        : Mohammed Nasiru Awal