Haramcin sanya niƙab | Labarai | DW | 08.03.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Haramcin sanya niƙab

Hukumar kare haƙƙin bil Adama a Turai ta nuna rashin amincewa da haramcin sanya niƙab.

default

Musulma sanye da hijab

A cikin wani jawabi da yayi, shugaban hukumar kare hakkin bil Adama a Turai yace ɗora haramcin sanya niƙab wani mataki ne da zai ƙara nuna wa mata danniya, amma ba ba su 'yancinsu ba. Thomas Hammarberg ya ƙara da cewa haramta sanya niƙab na zaman matakin yin shisshigi game da yadda mutun ke tafiyar da rayuwarsa. Akwai ƙasashen Turai da dama da suka haɗa da Austria, Denmark da kuma Holland da ke nazarin ɗora haramcin sanya niƙab. Hukumar wadda ba ta da wata alaƙa da Ƙungiyar Tarayyar Tuai an kafata ne a shekara ta 1949 domin kare haƙƙin bil Adama da kuma dimukuraɗiyya a Turai. Wannan jawabi dai yayi kiciɓis ne da bukin ranar mata da ake yi a faɗin duniya a yau. A watan Janairun da ya gabata sai da wani komiti na majalisar dokokin Faransa ya ba da shawarar gindaya haramci sanya niƙab a wasu keɓaɓɓun wurare. Wata ƙuri'ar jin ra'ayi da aka gudanar a ƙasar ta Faransa ta bayyanar da cewa kashi 74 daga cikin ɗari na al'umma sun goyi bayan ɗora haramcin sanya niƙab.

Mawallafiya: Halimatu Abbas

Edita: Muhammad Nasiru Awal