1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Har yau ana fama da ƙarancin abinci a duniya

October 15, 2010

Alƙaluma sun nuna cewar ƙasashe da dama dake yankin Sahel na Afirka na fama da ƙarancin abinci

https://p.dw.com/p/PfMj
Ƙarancin abinci a yankin SahelHoto: picture-alliance/ dpa

Yau dai zamu fara ne da rahoton jaridar Die Tageszeitung dangane da matsalar yunwa, wadda ta ƙi ci ta ƙi cinyewa a sassan duniya dabam-dabam duk da matakan taimakon da ake ɗauka. Jaridar ta ce:

"Ƙasashen Afirka dake kudu da hamadar Sahara su ne suka fi fama da raɗaɗin matsalar yunwar, kuma a halin da ake ciki yanzu ba wata alamar dake nuna cewar za a cimma burin nan na ƙarni a game da ƙayyade yawan masu fama da bala'in yunwa da misalin kashi hamsin cikin ɗari, kamar yadda aka ƙudurta nan da shekara ta 2015. Gaba ɗaya ƙasashe ashirin da tara ne matsalar ta shafa. Amma in ka fid da ƙasashen Haiti da Yemen ragowar ƙasashe ashirin da bakwai dukkansu na yankin Afirka ne a kudu da hamadar Sahara."

Niger Hungerkrise
Ƙasashe 27 matsalar ƙarancin abinci ta shafa a AfirkaHoto: AP

Ita kuwa jaridar Neues Deutschland cewa tayi har yau dai ana zaman tsammanin warabbuka ne dangane da ƙarni da aka kira wai na nahiyar Afirka, inda ta ci gaba da cewa:

"Ƙasashe goma sha bakwai ne suka samu 'yancin kansu a hukumance a nahiyar Afirka a shekara ta 1960, amma fa har yau nahiyar ta dogara ne kacokam akan cinikin ɗanyyun kayayyaki kuma hatta idan fasahin kayayyakin sun yi sama talakawa ba sa ganinta a ƙasa."

Jaridar ta ci gaba da cewar:

"A haƙiƙa ma dai Afirka ba ta yi amfani da rabin ƙarnin da ya gabata game da samun 'yancin kanta daidai yadda ya kamata ba. A wasu yankunan ma dai 'yan kama karya dake ɗanyyen mulki ne suka maye gurbin 'yan mulkin mallakan don ci da gumin talakawa. Ba shakka su ma ƙasashen yammaci suna da rabonsu na alhakin wannan mummunan ci gaba. Kuma ko da yake ana samun bunƙasar tattalin arziƙi, amma galibi sai an haɗa tare da keta haƙƙin ɗan-Adam a ƙasashe da dama na nahiyar."

Dossierbild 3 50 Jahre Unabhängigkeit in Afrika
Ƙasashe 17 suka samu 'yancin kai a Afirka shekaru 50 da suka wuceHoto: picture alliance/dpa

A karon farko bayan kimanin shekaru arbamenya an sake gabatar da 'yan fashin jiragen ruwa gaban kotun Jamus, kamar yadda mujallar Stern ta rawaito. Mujallar ta ce:

"'Yan Somaliya su goma da aka gabatar su gaban kotun, ana zarginsu ne da laifin fashin wani jirgin ruwan jaura daga Hamburg a cikin watan afrilun da ya wuce, wanda jim kaɗan bayan haka wasu dakarun ƙundumbala na ƙasar Netherlands suka sake ƙwato shi tare da cafke 'yan fashin."

A wani ci gaba kuma, wanda jaridar Die Tageszeitung take ganin yana tattare barazana, an yi wa baƙin haure 'yan ƙasar Zimbabwe takardun izinin zama a Afirka ta Kudu, in har sun yarda sun miƙa bayanansu ga mahukuntan Zimbabwe. Jaridar ta ƙara da cewar:

Simbabwe Südafrika Jacob Zuma in Harare Polizist
Afirka ta Kudu ta yi wa 'yan Zimbabwe alƙawarin izinin zama a ƙasarHoto: AP

"Lamarin dai yana tattare da walakin kuma da yawa daga 'yan ƙasar ta Zimbabwe sun yi imanin cewar wannan manufar wata dabara ce ta miƙa wa jami'an leƙen asirin shugaba Robert Mugabe bayanai a game da 'yan ƙasar dake zaune a Afirka ta Kudu. Domin kuwa ko da yake tun a farkon shekarar da ta wuce wata gwamnatin haɗin gambiza ke mulki a Zimbabwen, amma fa har yau hukumar leƙen asirin Mugabe tana nan daran daƙau kuma akwai ayar tambaya a game da zaɓan da ake shirin gudanarwa shekara mai zuwa saboda har yau ba a yi canje-canjen da ake buƙata game da zaɓen a daftarin tsarin mulkin ƙasar ba."

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Mohammed Nasiru Awal