1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Har yanzu Sharon na cikin mawuyacin hali na rashin lafiya

Har yanzu FM Isra´ila Ariel Sharon na cikin wani mawuyacin hali na rashin lafiya bayan aikin tiyata na gaggawa da aka yi masa don cire wani bangare na hanjinsa a jiya asabar. Rahotannin daga asibitin Hadassah dake birnin Kudus sun ce har yanzu FM na cikin wata doguwar suma tun bayan da yayi fama da bugun jini a farkon watan janeru. Daraktan asibitin na Hadassah Shlomo Mor-Yosef ya ce bayan an samu nasarar yin tiyatar kuma rayuwar Sharon ba ta fuskantar wata barazana, amma babbar matsalar su ita ce doguwar sumar da yake ciki. Kwararru a fannin kiwon lafiya ba su da kyakkyawan fatan cewa Sharon mai shekaru 77 a duniya zai farfado bayan ya yi fama da zubar jini a kwakwalwarsa a ranar 4 ga watan janeru.