Har yanzu Mr Sharon na cikin mawuyacin hali | Labarai | DW | 10.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Har yanzu Mr Sharon na cikin mawuyacin hali

Rahotanni daga asibitin da aka kwantar da Faraministan Israela, Mr Ariel Sharon sun nunar da cewa har yanzu faraministzan na cikin mawuyacin hali, a yayin da likitocin ke kokarin dawo dashi cikin hayyacin sa, bayan sumar dashi da suka yi don gudanar da aiki a cikin kwakwalwar sa.

Likitocin dake lura da Mr sharon sun tabbatar da cewa ci gaba da dawo dashi cikin hayyacin nasa ka iya daukar kwanaki, bisa irin matsanancin halin da yake ciki a halin yanzu.

A dai jiya litinin, bayanai sun nunar da cewa a karon farko Mr Sharon yayi numfashi da kansa, wanda hakan ke nuna alamun samun ci gaba a game da fafutikar da likitocin keyi don ceto ran sa.

Idan dai an iya tunawa, an kwantar da Mr sharon ne a asibitin bayan ya fuskanci bugun jini mai karfin gaske, wanda ya haifar masa da tsinkewar jini a cikin kwakwalwar sa.