Har yanzu jiragen saman Isra´ila na barin wuta a kudancin Libanon | Labarai | DW | 05.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Har yanzu jiragen saman Isra´ila na barin wuta a kudancin Libanon

Jiragen saman yakin Isra´ila sun sake kai farmaki akan babban birnin Lebanon. Kamar yadda ´yan sanda a birnin suka nunar an yi ruwan bama-bamai a unguwannin dake wajen kudancin birnin na Beirut, inda ya kasance sansanin mayakan Hisbollah. Rahotanni sun ce an ji karar fashewar abubuwa akalla guda 6. A can birnin Tyre mai tashar jiragen ruwa dake kudancin Libanon jiragen saman yakin Isra´ila sun kai hare hare. A jiya juma´a dai wani hari ta sama da Isra´ila ta kai a kusa da garin Qaa dake arewa maso gabashin Libanon a dab da kan iyakarta da Syria, ta halaka akalla fararen hula 26 yayin da wasu 20 suka samu raunuka. Hazalika jiragen saman yakin Yahudun Isra´ila sun lalata gadoji guda 4 a arewacin Beirut, abin da ya kawo cikas ga jigilar kayan agaji. Ita kuma a nata bangaren Husbollah ta harba rokoki da dama zuwa birnin Hadera na Isra´ila mai tazarar kilomita 80 daga kan iyakar ta da Libanon.