Har yanzu babu wani ci-gaba a taron sauyin yanayi na Bali | Labarai | DW | 14.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Har yanzu babu wani ci-gaba a taron sauyin yanayi na Bali

Ana ci-gaba da ja-in-ja a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya kan sauyin yanayi a birnin Bali na kasar Indonesia a dangane da rage yawan gurbataccen hayaki mai ɗumama doron ƙasa. Kawo yanzu minitoci 40 da suke shawartawa ciki har da ministan kare muhalli na Jamus, Sigmar Gabriel sun kasa cimma wani tudun dafawa. Har izuwa yanzu Amirka ta ƙi amincewa da kudurorin da ƙasashe masu arzikin masana´antu suka yanke na rage fid da hayakin Carbon Dioxide mai gurbata yanayi. Su ma ƙasashen Kanada da Rasha da Japan da kuma Australiya suna nuna ɗari-ɗari. Kungiyar tarayyar Turai ta yi kira da rage yawan gurɓataccen hayakin da kashi 25 zuwa 40 cikin 100 kafin shekara ta 2020. Duk da wannan tarnaƙin dai dukkan sassan da abin ya shafa sun nuna shirin cimma wani daidaito.