Har yanzu Ariel Sharon na cikin mawuyacin hali a asibiti | Labarai | DW | 07.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Har yanzu Ariel Sharon na cikin mawuyacin hali a asibiti

Bayan aikin tiyata na 3 likitocin Isra´ila na kokarin farfado da FM Ariel Sharon. Bayan sun shafe sa´o´i sama da 5 suna yi masa tiyata shugaban asibitin dake birnin Kudus Shlomo Mor Josef ya bayyana halin da Sharon ke ciki da cewa ya dan kyatattu amma har yanzu yana kwance rai hannun Allah. Mista Josef ya ce yanzu jini ya bar zuba a cikin kwakwalwar FM na Isra´ila mai shekaru 77 a duniya. Ko da ya ke gidan telebijin Isra´ila ya rawaito cewar da alamu FM ka iya farfadowa, amma gidajen radiyon kasar sun ce zubar jinin da kwakwalwarsa ta yi sakamakon mutuwar jikin da ya fuskanta a ranar laraba, ba za´a iya warkar da kwakwalwar ba. To amma likitan da ke masa jiyya Felix Umansky ya musanta haka.