Har yanzu ana take hakkin bil adama a Darfur | Labarai | DW | 02.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Har yanzu ana take hakkin bil adama a Darfur

Wakiliyar MDD ta musamman kann kare hakkokin bil adama a Sudan Sima Samar tace har yanzu ana ci gaba da take hakkin bil adama a kasar.

Bayan rangadinta na kwanaki hudu Samar ta baiyanawa taron manema labarai cewa ta tattauna kann batutuwa da dama tsakaninta da jamian Sudan ciki har da batun tsare yan jarida da yan adawa.

Samar ta koka da cewa har yanzu baa bude kafa hukumar kare hakkin bil adama ba a arewacin kasar kamar yadda ake da shi a kudancin Sudan.

A watan daya gabata hukumar kare hikkin bil adama ta MDD tayi Allah wadai da ci gabva da akeyi da kashe kashe da fyade a lardin Darfur.

A halinda ake ciki kuma rahotann sunce akalla mutane 100 suka rasa rayukansu cikin wannan mako a a yankin Diyala a Darfur cikin fada tsakanin yan Janjaweed da mazauna yankin.