1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Har yanzu ana fama da zubar da jini a Iraki

August 5, 2006
https://p.dw.com/p/Bunm

Akalla mutane 24 aka kashe a ci-gaba da tashe tashen hankula da ake fama da su a fadin kasar Iraqi. ´Yan kallon wasan kwallon kafa kimanin 10 aka kashe sannan aka yiwa sama da 12 rauni a wani harin kunar bakin wake da aka kai da mota a lokacin wata karawa a garin Hadhra dake arewacin Bagadaza. A kuma birni Mosul dake arewacin Iraqi, an yi musayar wuta bayan wani bam da aka dana cikin mota ya halaka ´yan sanda 4. Harbe harben da aka yi ya bazu zuwa wasu unguwannin, wanda ya yi sanadiyar rayukan ´yan tawaye su 8. Bayan sallar juma´a a jiya dubun dubatan ´yan shi´a daga ko-ina cikin Iraqi sun yi wani gangami don nuna goyon baya ga kungiyar Hisbollah. A kuma can birnin San Diego na Amirka an caji wasu sojojin Amirka 6 da laifin cin zarafin wani dan Iraqi a garin Hamdania. Sojojin sun yiwa mutumin dukar kawo wuka, har sai da ya ce ga garinku nan. Uku daga cikin sojojin kuma ana zarginsu da yiwa wani dan Iraqi kisan gilla a wannan gari.