1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Har yanzu ana fama da zubar da jini a Iraki

Zainab A MohammedAugust 24, 2006
https://p.dw.com/p/Bu5p

Mutane 14 suka rasa rayukansu wayewar garin yau ,kana wasu da dama sun raunana, a harin boma boman motoci daban daban guda 3,a bagadaza a ayau.Sanarwar data fito daga maaikatar tsaron Irakin na nuni dacewa mutane biyu sun gamu da ajalinsu,ayayinda wasu 9 suka jikkata sakamakon tarwatsewar wata mota da aka jibge boma bomai acikinta a unguwar Jadida,kusa da gunduwar Sadr a bagadazan ayau.Kazalika wasu mutane biyu sun rasa rayukansu,kana 4 sun jikkata ,wadanda suka hadar da yansanda 2,a lokacinda bomb ya fashe a wata mota dake tsaye a unguwan yan sunni dake Adhamiyah.

Kana sojojin Amurka guda biyu sun bakunci Lahira .Bugu da kari sojin Irakin 3 suma sun gamu da ajalinsu ayau din,lokacinda ayarin motocinsu yabi kan Bomb da aka dasa a gefen hanya a garin Buhriz dake arewacin Bagadaza.A garin Baquba kuwa,tashin bomb a wata motar bus ya kasha yan sanda 3 da matukin motar.Kazalika wasu jamian yansandan biyu sun rasa rayukansu sanadiyar bi takan boma bomai dasassu.