1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Har yanzu ana fama da rikicin siyasa a Kenya

January 4, 2008
https://p.dw.com/p/CkNK
Babbar jam´iyar adawa a ƙasar Kenya ta yi kira da a sake gudanar da sabon zaɓen shugaban ƙasa. Wannan buƙata ta zo ne a matsayin martani ga sake zaɓen shugaba Mwai Kibaki da ake takaɗɗama a kansa, wanda kuma ya janyo munanan tashe tashen hankula a ƙasar. Dan takarar ´yan adawa Raila Odinga da magoya bayansa da suka buƙaci a sake shirya sabon zaɓen nan da watanni uku, sun yi zargin tabka maguɗi a zaɓen shugaban kasar da aka gudanar a makon da ya gabata. A yau juma´a ´yan adawa sun ce zasu ci-gaba da zanga-zanga a babban birnin kasar wato Nairobi yayin da aka girke dubban ´yan sandan kwantar da tarzoma a ciki da wajen birnin. Shugaba Kibaki yayi kira da a kwantar da hankula sannan yayiwa abokanen adawarsa tayin sasantawa bayan tashe-tashen hankulan da aka fuskanta a jiya alhamis.