Har yanzu akwai bambamcin ra´ayi dangane da kafa gwamnatin Falasdinawa | Labarai | DW | 05.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Har yanzu akwai bambamcin ra´ayi dangane da kafa gwamnatin Falasdinawa

Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas ya gudanar da wata tattaunawa da nufin kafa wata gwamnatin hadin kan kasa da FM Ismail Haniya a birnin Gaza. To sai dai har yanzu ba´a cimma matsaya daya ba game da manufar da aka sanya a gaba. Kungiyar Hamas ta Haniya dake jan ragamar mulki da kungiyar Fatah dake karkashin jagorancin Abbas sun sanya hannu kan yarjejeniyar raba madafun iko a taron da suka yi a Saudiyya a cikin watan da ya gabata. Ko da yake yarjejeniyar ta kawo karshen rikicin tsakanin kungiyoyin biyu amma ba ta cimma bukatun kasashen yamma don a dage takunkuman kudi da na ba da tallafi ga gwamnatin Hamas ba. Manyan jami´an Falasdinawa sun ce za´a dauki kwanaki masu yawa ana gudanar da wannan tattaunawa kuma akwai bambamce bambamcen ra´ayi akan muhimman batutuwa.