Har tsugune bata kare ba a Iraq | Siyasa | DW | 26.10.2004
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Har tsugune bata kare ba a Iraq

A daren jiya dakarun Amurka sunyi dirar mikiya a falluja a Iraq a cifaba da farautar yan tawayen Abu Musa Alzarqawi

Biyu daga cikin Sojojin Amurka a Falluja

Biyu daga cikin Sojojin Amurka a Falluja

A dangane da dauki ba dadin dake wanzuwa a can kasar iraq a birnin falluja a yau dakarun Amurka sun cigaba da dirar mikiya a birnin tare da datse duk wasu hanyoyin da suka shiga cikin birnin a yau talata .Wadanda suka ganewa idansu yarda lamarin ke faruwa kuwa sun tabbatar da cewa dakarun sun shiga cikin birnin da muggan maskamai da tankunan yaki a wani mataki na farautar magoya bayan Abu musa Alzarqawi madugun yan tawayen kasar .Wata majiya na cewa dakarun dai sunyi sansani a cikin wani gidan da babu kowa a cikinsa baya ga yin kawanya a birnin baki daya ..Tun daga daren jiya dai fararen hula suka fice daga cikin birnin bisa tsoron cewa wani kazamin fadan ka iya barkewa a tsakanin bangarorin biyu ..Majiyar dai na cewa gwamnatin rikon kwarya nackokarin ganin cewa komai ya lafa kafin a gudanar da zabe a farkon watan sabuwar shekara idan Allah ya kaimu ..Bugu da kari majiyar data fito daga dakarun Amurka a yau tace ta kai wannan kazamin farmakin ne tun daga daren jiya inda suka kashe daya daga cikin manyan jakadun Abu Musa madugun yan tawayen .To sai dai amurkan bata bayyana sunan wannan mutumin ba kamar yarda take ikirari .Mazauna birnin dai sun tabbatar da cewa an lalata wasu gidaje 4 a farmakin na jiya .Wannan dai shine karo na biyu da dakarun na Amurka sukai shelar kisan magoya bayan madugun yan tawayen batare da bayyana suna ba ..To sai dai a cewar ministan harkokin kasashen ketare na kasar ta Iraq Hoshiyar Zebari yace ana daukar matakai na tuntubar juna domin warware rikicin baki dayansa a falluja a cikin kasar ta iraq .Yace idan baa mantaba a tashi baram baram a wata tattaunawa da jamian Amurka a falluja a watan Afrilun wannan shekara wanda kuma zaa sake wannan batu a tsakanin yan kasar zalla ..A daura da wannan halin dai mazauna yankin sun karyata zargin cewa suna bayar da mafaka ga Abu musa domin cigaba da tayar da zaune tsaye .Sun dai bukaci cewa basa son gasnin koda dan kasar Amurka daya a cikin birnin idan har ana bukatar cimma daidaito a tsakanin bangarorin biyu ..Tun ba yanzu ba dai kungiyar dake da nasaba da abu musa ke ikirarin gudanar da yin garkuwa da bakin dake cikin kasar baya ga fillewa wasu Kawuna .Idan dai baa mantaba koda a jiya sai da yan tawayen suka kashe wasu Kuratan sojoji da suka kammala horo su 50 wanda hakan ya haifar da bayar da wani umarni daga Pm kasar Iyad Allawi na gudanar da bincike mai zurfi ko yan tawayen nada masaniyar wadannan sohjojin dake kann hanyarsu ta komawa gida na hutun dan gajeran lokaci kafin su fara aiki a cikin kasar .Kodsa a yau kuwa sai da wasu bama Bamai suka fashe a Baguba inda wani jamiin yan sanda ya rigamu guidan gaskiya

 • Kwanan wata 26.10.2004
 • Mawallafi Mansour bala Bello
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvfC
 • Kwanan wata 26.10.2004
 • Mawallafi Mansour bala Bello
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvfC