Har kawo yanzu tsugune bata kare ba a Iraq | Siyasa | DW | 21.10.2004
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Har kawo yanzu tsugune bata kare ba a Iraq

A can Iraq har yanzu bata sake zane ba a cigaba da dauki ba dadi a tsakanin yan tawaye da dakarun amurka .Gwamnatin Britaniya na cigaba da tattaunawa domin karin dauki ga yankin falluja

Hayaki ya turnuke a wani gidan da yaki ya rutsa dashi

Hayaki ya turnuke a wani gidan da yaki ya rutsa dashi

A wata sanarwa da maaikatar cikin gida a iraq a yau ta sanyawa hannu tace an bindige wasu jamian tsaro su biyu a bagadaza daga wasu yan kunar bakin waken dake cikin wata mota.Bugu da kari a cikin wannan yamutsin ya rutsa da wata mace kamar yarda kakakin wannan maaikata adnan Abdulrahman ya shaidar a yau alhamis .A hannu guda kuma wata majiya na cewa wasu yan bindiga dadi sun harbe wasu mutane biyu tare da raunata wasu da dama .A yanzu haka dai ayyukan yan tawayen sunfi mayar da hankali ne ga jamian tsaro a cigaba da dauki ba dadin dake tsakanin Amurka da yan tawayen kasar ta iraq .A dangane da wannan halin da ake ciki ne gwamnatin britaniya ke daukar matakai na jibge dakarunta a wuraren da yakin ya kazanta kamar yarda Amurka ta bukata tun da fari .To sai dai hakan ya sake jefa Pm tony Blair cikin wata dambarwar siyasa a cikin gida .A dangane da haka ne kakakin Pm kasar yace tun a jiya ministocin kasar suka amince da tabbatar da wannan batu domin samun nasarar gudanar da zabe a cikin kasar ta iraq wanda dole ne a kare martabar yan kasar daga barazanar tsaro musamman bisa ayyukan yan tawaye a cikin kasar .a yammacin yau dai Ministan tsaro zai gana da yayan majalisar dokokin kasar domin karin haske kann halin da ake ciki a iraq tare da bukatar da Amurka ta nema na karin dakarun Britaniya zuwa yankunan da sukafi tsanani a iraq ..a yanzu haka dai ana bukatar a kalla dakarun Britaniya 650 daga yankin basra zuwa falluja domin kai dauki ga dakarun Amurka a wani mataki na murkushe yan tawayen abu musa alzargawi .Wata majiya dai na cewa an dauki wannan matakin ne domin tabbatar da nasarar gudanar da sabon zabe a iraq a farkon shekarar mai kamawa idan allah ya kaimu ..To sai dai a wata sabuwa koda ga yayan jamiyyar labor ta Pm Blair na nuna adawa da wannan batun aikewa da karun zuwa yankunan da sukafi muni a cikin kasaar ta iraq baya ga jamiyyun adawa .Dakarun Britaniya dai na jibge ne a basra inda babu wani yamutsi a halin yanzu .wAta majiya na cewa tun da aka fara yaki da iraq dakarun britaniya 68 ne kacal suka mutu idan aka kwatanta da dakarun amurka sama da dubu daya .to sai dai masana ilmin siyasa na kallon cewa wannan matakin wata akarkashiya ce dake neman bayar da goyan baya ga shugaba bush daga gwamnatin ta Britaniya domin murkushe yamutsin daa halin yanzu ke wakana a iraq kasancewa yakin neman zabe a amurka ya dogara ne kacokam ga halin rayuwa a iraq .To sai dai Gwamnatin Blair ta musanta wannan batun da cewa babu kanshin siyasa a cikinsa .

 • Kwanan wata 21.10.2004
 • Mawallafi Mansour Bala Bello
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvfL
 • Kwanan wata 21.10.2004
 • Mawallafi Mansour Bala Bello
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvfL