Har ila yau ba a gano mutane 15 ba karkshin rufin ginin da ya burme a kasar Poland. | Labarai | DW | 30.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Har ila yau ba a gano mutane 15 ba karkshin rufin ginin da ya burme a kasar Poland.

`Yan sandan kasar Poland, na ta kokari, tare da yin amfani da karnuka wajen sunsuno sauran mutanen da har ila yau ba a gano su ba tukuna, a karkshin rufin zauren nunin nan da ya burme a kansu a garin Katowice tun ran asabar. A halin da ake ciki dai, hukumar `yan sandan birnin ta ce fatar gano wasu mutanen da ransu karkashin tarkacen na ta kara dusashewa. Mutane 67 ne dai aka ce kawo yanzu sun rasa rayukansu a wannan hadarin, sa’annan wasu dari da 50 kuma suka ji rauni. Jami’an kiwon lafiya a garin na Katowice, sun ce mai yiwuwa za a sami karin mutanen da suka rasa rayukansu, idan aka yi la’akari da munanan halayen da wasu daga cikin wadanda suka ji raunin ke ciki a yanzu. Mahukuntan kasar ta Poland dai sun kaddamad da kwanaki uku na juyayi a duk fadin kasar baki daya.

Tuni dai, an fara gudanad da bincike don gano dalilan da suka janyo burmewar rufin zauren nunin. Da farko dai, qan yi zaton cewa nayuin dusar kankara da ke kann rufin ne ya janyo burmewarsa.