Hankalin Turai ya karkata ga zaben Italiya | Labarai | DW | 04.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hankalin Turai ya karkata ga zaben Italiya

Jama'ar Italiya na kada kuri'a a zaben raba gardama domin yanke hukunci kan yiwuwar gyaran kundin tsarin mulki da ma sauya fasalin gwamnati

Jama'ar Italiya na kada kuri'a a zaben raba gardama kan kundin tsarin mulki. Firaministan kasar Matteo Renzi tare da mai dakinsa sun kada kuri'un su a Pontassieve kusa da birnin Florence.

Jigon kuri'ar raba gardamar shine karfafa karfin iko a hannun gwamnatin tarayya ta hanyar rage tasirin majalisar dokoki da kuma gundumomi. Hankalin kasashen Turai dai ya karkata ga wannan zabe wanda ake kallo na iya yin tasiri ga makomar kungiyar tarayyar Turan EU.

Masu goyon bayan amincewa da gyaran kundin tsarin mulkin na cewa hakan zai fi samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasa, yayin da wasu ke baiyana cewa abin da Firaministan ke bukata ya saba tafarkin dimokradiyya. Kuri'ar raba gardamar dai har ila yau na zama zakaran gwajin dafi ga Mr Renzi wanda ya yi alkawarin yin murabus idan masu zabe suka yi fatali da kudirin.