1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Haniyey ya ce a shirye ya ke yayi murabus

A wani labarin kuma FM Falasdinawa Ismail Haniyeh na kungiyar Hamas ya ce a shirye ya ke yayi murabus, muddin yin haka zai sa kasashen yamma sun kawo karshen takunkumin ba da tallafi da suka sanyawa gwamnatinsa. Wadannan kalaman na sa sun zo ne bayan tattaunawar kafa wata gwamnatin hadin kan kasa da ya yi da shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas a birnin Gaza. Haniyeh ya ce ana samun ci-gaba a tattaunawar kuma yayi fatan cewa ana iya nada sabuwar majalisar ministoci cikin makonni 3 masu zuwa. Isra´ila da kasashen yamma sun kakabawa hukumar mulkin cin gashin kan Falasdinawa takunkumai saboda kin da Hamas ta yi na amincewa da ´yancin wanzuwar Isra´ila, yin watsi da tashe tashen hankula da kuma kin girmama yarjeniyoyin da aka kulla tsakanin Isra´ila da Falasdinu.