Haniyeh ya koma Gaza amma ba tare da ko sisin kwabo daga ketare ba | Labarai | DW | 15.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Haniyeh ya koma Gaza amma ba tare da ko sisin kwabo daga ketare ba

Kungiyar Hamas ta ce harbin da aka yi kan ayarin motocin FM Falasdinawa Isma´il Haniyeh a kan iyakar Gaza, wani yunkuri ne na halaka shi daga abokiyar adawa wato Fatah. An budewa ayarin motocin Haniyeh wuta lokacin da aka ba shi izini ya tsallake kan iyakar, bayan an hana shi yin haka da farko. An kashe mai tsaron lafiyar guda sannan aka jiwa dansa rauni a tsallaken iyakar ta Rafah. Da farko Isra´ila ta hana Haniyeh tsallake kan iyakar da miliyoyin daloli da ke tare shi. Isra´ila ta ce kudaden na taimako musamman daga Iran za´a yi amfani da su ne wajen tallafawa ayyukan ta´addanci a kan ta. A karshe an amince ya wuce bayan da ya bar wadannan kudade a hannun masharwartansa a Masar.