1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Haniya yayi kira ga Falasdinawa da su kauracewa kuri´ar raba gardama

June 10, 2006
https://p.dw.com/p/Buub
Duk da hare haren da Isra´ila ke kaiwa, ana sa rai shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas zai kira kuri´ar raba gardama akan kafa wata kasar Falasdinawa mai makwabtaka da Isra´ila a ranar 31 ga watan yuli. Sai dai FM Falasdinawa Isma´ila Haniya yayi kira ga ´yan kasar da su kauracewa kuri´ar raba gardamar da shugaba Abbas ke shirin gudanarwa. Haniya ya fadawa mujallar Der Spiegel ta nan Jamus cewa Abbas bai da ´yancin shirya wannan zabe. Haniya ya sake yin fatali da bukatar gamaiyar kasa da kasa game da amincewa da wanzuwar kasar Isra´ila kana kuma ya yi watsi da tashe tashen hankula. A ra´ayin FM Isra´ila Ehud Olmert kuri´ar raba gardamar ba zata ba da wata gudummawa ba wajen warware rikicin yankin GTT. Olmert ya ce kuri´ar wata harka ce ta cikin gida tsakanin kungiyoyin Falasdinawa biyu.