1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hana sayad da man fetur a kan tituna a Benin ta janyo wata mummunar adawa.

June 18, 2006
https://p.dw.com/p/ButT

Ƙasar Jumhuriyar Benin, ta ɗaga lokacin aiwatad da dokar haramta sayad da man fetur a bakin tituna har zuwa makwanni biyu nan gaba, saboda yajin aikin da masu sayad da man fetur ɗin suka yi, abin da ya janyo dogayen layi a gidajen sayad da man. Gwamnatin ƙasar, ta haramta sayad da man fetur din cikin gwangwani a bakin ttituna ne, bayan da wani haɗarin da ya auku a watan jiya, ya halakad mutane 60, mazauna ƙauyen Porga, mai nisan kimanin kilomita ɗari 5 a arewacin Cotonou, babban birnin ƙasar. Haɗarin dai ya auku ne, yayin da wata tankar mai ta yi bindiga, a daidai lokacin da ’yan ƙauyen ke satar mai daga motar.

Masu sayad da man dai, sun ce ba su da wani zaɓi, idan suka bar wannan sana’ar, saboda ana fama da yawan marasa aikin yi a ƙasar. Yajin aikin dai, ya janyo ƙaranci da ma rashin mai a wasu gidajen sayad da man fetur a babban birnin.

Shugaban ƙasar, Yayi Boni, ya ce zai gana da wakilan masu kasuwancin man fetur ɗin, don a iya samad da wata madafa ta warware wannan matsalar.