Hamid Karzai ya fara waádin mulki karo na biyu | Siyasa | DW | 19.11.2009
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Hamid Karzai ya fara waádin mulki karo na biyu

Shugaba Karzai yayi kira ga yan Taliban su ajiye makamansu domin haɗa hannu da gwamnati wajen cigaban kasa

default

Bikin rantsar da Shugaban Afghanistan Hamid Karzai.

Shugaban Afghanistan Hamid Karzai domin fara waádin mulki karo na biyu. Bikin rantsuwar wanda aka gudanar da shi a fadar gwamnati a birnin Kabul ya sami halartar shugabanni da mashahuran mutane dasa sassa daban daban na duniya.

Sanye da kayan gargajiya na alada da kuma Falmaran a kafaɗarsa shugaba Karzai mai shekaru 52 da haihuwa ya karɓi rantsuwar kama aiki a ƙwarya ƙwaryar bikin da aka nuna ta akwatunan talabijin a faɗin ƙasar. " A jawabinsa Karzai yayi alƙawarin yin aiki tsakani da Allah da kare martaba da cigaban addinin musulunci da kuma yin biyayya ga kundin tsarin mulki da sauran dokoki na ƙasar Afghanistan da kuma aiwatar da su.

Bayan da ya karɓi tasa rantsuwar ce sai kuma ya jagoranci rantsar da mataimakansa biyu Mashal Mohammed Qasim Fahim da kuma Mohammed Karim Khalili wadanda dukkaninsu sun fito ne daga manyan ƙabilun ƙasar.

Shugaban ƙasar Pakistan Asif Ali Zardari da sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton tare da Ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle da takwarorinsa na Faransa da Buritaniya na daga cikin waɗanda suka halarci bikin rantsar da shugaban.

A jawabinta Hillary Clinton ta yi bayani da cewa " A yanzu akwai gagarumar dama ga shugaba Karzai da gwamnatinsa su samar da sabon yanayi ga jamaár Afghanistan domin nunawa a zahiri cewa zaá sami sauyi mai maána da zai kawo kyautatuwar rayuwar alumar wannan gagarumar ƙasa.

An keɓe ranar Alhamis a matsayin ranar hutu ce a faɗin ƙasar yayin da kuma aka tsaurara matakan tsaro a ko ina bisa fargabar harin yan Taliban musamman akan hanyar da ta haɗe zuwa fadar gwamnati a birnin Kabul. Bugu da ƙari an soke tashi da saukar jiragen saman fasinja.

Karzai wanda ke fuskantar gagarumin ƙalubale da suka haɗa da tarzomar yan Taliban, ya yi kira ga yan tawayen Taliban ɗin da su ajiye makamansu su komo ga rayuwar alúma ta yau da kullum domin bada gudunmawarsu ga cigaban ƙasa.

" Tsawon shekaru 30 jamaármu suke ta fafutuka domin tabbatar da ɗorewar zaman lafiya. Yana mai cewa zaman lafiya da tsaro ba zasu samu ta hanyar yaƙi ko kuma tarzoma ba".

Shugaban na Afghanistan ya ƙara da cewa suna maraba da yan ƙasar waɗanda basu da alaƙa da ƙungiyoyin yan tarzoma na ƙasa da ƙasa. Suna kuma marhabun da dukkan waɗanda suka zaɓi kwanciyar hankali da lumana. Yace gwamnati a shirye take a ko da yaushe taimaka musu.

Hamid Karzai ya kuma zayyana manufofin da gwamnatinsa zata aiwatar a waádin mulkin na biyu, inda yace zai kira taron majalisar alúmomi ko kuma Jirga domin tsara yadda zaá aiwatar da sulhu da yan tawaye.

A waje guda dai Karzai wanda ada ya kasance majidaɗin turawan yamma, a yanzu tauraruwarsa ta dusashe saboda gazawarsa wajen tabbatar da tsaro a ƙasar da kuma cin hanci da rashawa da suka mamaye mulkinsa na shekaru biyar da suka wuce.

Karzai ya kuma yi kakkausar suka ga kafofin yaɗa labarai waɗanda yace sun yi ƙarin gishiri game da matsalar cin hanci da rashawa a gwamnatinsa. Ya ci alwashin cewa wakilan sabuwar majalisar Ministoci da zai naɗa zasu kasance ƙwararun jamiai kana zaá ɓullo da sabuwar doka wadda a ƙarƙashinta dukkanin manyan jamián gwamnati zasu baiyana kadarorinsu da dukkan abinda suka mallaka.

Mawallafi :- Abdullahi Tanko Bala

Edita :- Umaru Aliyu

 • Kwanan wata 19.11.2009
 • Mawallafi Abdullahi Tanko Bala
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/KbJR
 • Kwanan wata 19.11.2009
 • Mawallafi Abdullahi Tanko Bala
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/KbJR