Hamas ta zabi Isma´il Haniyeh a matsayin saban Pramistan Palestinu | Labarai | DW | 17.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hamas ta zabi Isma´il Haniyeh a matsayin saban Pramistan Palestinu

Kungiyar Hamas da ta lashe zaben yan majalisun dokokin Palestinu a watan Janairu da ya wuce ta zabi Isma´il Haniyeh a matsayin saban Praminista.

Zabbabun yan majalisu dokoki kasar ne su ka yanke wannan shawara wani zama taro da su ka yi ranar jiya alhamis a Rammallah.

Ranar asabar mai zuwa za su gabatar da sunan saban Praministan ga shugaban kasa Mahamud Abbas.

Zaben Isma´il Haniyeh a matsayin Praministan Hamas, bai baiwa masharahanta a yankin mamaki ba, kasancewar sa, daya daga na hannun damar tsofan shugaban kungiyar Scheik Yacine Ahmed da rundunar Israela ta kashe a shekara ta 2004.