1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hamas ta yi watsi da bukatar girke dakarun duniya a Zirin Gaza

Kungiyar Hamas ta masu kishin Islama ta yi watsi da bukatar da shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas ya nuna dangane da tura dakarun kasa da kasa a Zirin Gaza. Hamas mai mulki a Zirin na Gaza ta ce za´a kaiwa wadannan dakaru hari idan aka girke su a yankin. Bayan ganawar da ya yi da sabon shugaban Faransa Nikolas Sarkozy a birnin Paris, Abbas ya nuna cewa girke wata rundunar kasa da kasa a Zirin Gaza ka iya tabbatar da kwanciyar hankali a yankin tare da gudanar da zabe na gama gari.