Hamas ta yi tir da sabuwar gwamnatin da Mahmud Abbas ya rantsar | Labarai | DW | 17.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hamas ta yi tir da sabuwar gwamnatin da Mahmud Abbas ya rantsar

Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas ya rantsad da wata sabuwar gwamnatin gaggawa a wani buki da aka yi a hedkwatarsa dake birnin Ramallah na Gabar yamma da kogin Jordan. Jim kadan bayan haka ya rusa bangaren soji na kungiyar Hamas. Abbas ya nada majalisar ministocinsa mai membobi 11 bayan ya rusa gwamnatin hadin kann kasa wadda ta kunshi ´ya´yan jam´iyar Hamas da na Fatah. To sai dai kakakin Hamas Fauzi Barhom ya yi watsi da sabuwar gwamnatin yana mai cewa babu wata hujja ta doka da ta lamunci wannan gwamnati.

Insert O-Ton Barhom:

„Mu ´yan Hamas mun yi tir da wannan gwamnati da kuma matakin da aka dauka na korar halattacciyar gwamnatin al´umar Falasdinu. Wannan gwamnati wadda shugaba Abbas ya bawa Salam Fayad ba ta dace da doka da kuma kundin tsarin mulki ba.“