1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hamas ta yi kira ga gudanad bincike kan makaman da Isra’ila ta tura wa Ƙungiyar Fatah.

June 18, 2006
https://p.dw.com/p/ButV

Ƙungiyar Hamas, ta yi kira ga Majalisar Falasɗinawa da ta gudanad da bincike kan tura makamai da Isra’ila ta yi, ga dakarun da ke nuna biyayya ga Ƙungiyar Fatah ta shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas. A cikin wani rahoton da jaridar nan ta Jerusalem Post ta buga, ta ce kusan manyan bindigogi ƙirar M-16, dubu da harsashensu da dama ne Isra’ilan ta tura wa dakarun Mahmoud Abbas, a makon da ya gabata, a daidai lokacin ta ake ta ƙara samun hauhawar tsamari, tsakanin rukunin shugaban Falasɗinawan da Ƙungiyar Hamas mai jan ragamar mulki. Tuni dai, wannan hauhawar tsamarin ta janyo mummunar fafatawa, tsakanin dakarun Hamas ɗin da na Ƙungiyar Fatah ta Mahmoud Abbas, a yankin zirin Gaza, inda ɓangarorin biyu ke ta gwaggwarmayar tabbatad da ikonsu kan jami’an tsaron Falasɗinawan. Ita dai Hamas ta ce, tura makaman da Isra’ila ta yi, wato wani shiri ne na janyo yaƙin basasa a yankunan Falasɗinawan.