Hamas ta naɗa majalisar Ministoci | Labarai | DW | 20.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hamas ta naɗa majalisar Ministoci

Hamas ta miƙa sunayen yan majalisar ministoci da ta naɗa ga shugaban hukumar gudanarwar Palasɗinawa Mahmoud Abbas. P/M mai jiran gado Ismaila Haniya yace sabbin ministocin 24 sun haɗa da mace ɗaya da Krista ɗaya da kuma wasu manyan jamiái biyu na ƙungiyar Hamas, waɗanda suka haɗa da Mahmud al-Zahar da kuma Said Siam. Majiyoyi sun baiyana cewa Zahar shi ne zai rike mukamin Ministan harkokin waje, yayin da kuma Siam zai shugabanci maáikatar alámuran cikin gida. Jamíyar Fatah ta ƙi amincewa da shiga gwamnatin hadin kan kasar karkashin jagorancin Hamas. Shugaban Palasdinawa Mahmoud Abbas ya ce zai kira taron hukumar gudanarwar Palasɗinawa domin tattaunawa a game da sunayen ministocin da aka gabatar. Tuni dai Israila ta baiyana cewa ba za ta yi hulɗa da gwamnatin Hamas ba wadda ta baiyana da cewa kungiya ce ta yan taádda.