Hamas ta maida martani ga Turai da Amurika | Labarai | DW | 31.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hamas ta maida martani ga Turai da Amurika

Kasashe 5 masu kujerun dindindin a komitin sulhu na Majalisar Dinkin Dunia, sun kudurci gurfanar da Iran ,gaban komitin , bayan taurin kan da ta nuna, na kin watsi da shirin ta, na kera makaman nuklea.

Wakilin Iran a tantanawar harakokin Nuklea Ali Larjani, ya sannar cewa, wannan mataki da kasashen su ka dauka, ba zai sa Iran ta karaya ba, ko tab yi kasa a gwiwa a game da akidar da ta sa gaba.

Kazalika,Ali Karjani,yayi kira ga kasashen Turai, da ke cikin wannan tantanawa, da su lashe amen su, domin gurfanar da Iran gaban komitin Sulhu, ba shi ne hanya ma fi dacewa ba,ta warware wannan matasala.

Ranar alhamis, idan Allah ya kai mu, wakilai a hukumar yaki da yaduwar makaman nukela, za su zaman taro, domin masanyar ra´ayoyi, a game da saban salan da rikicin ya dauka.