1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hamas ta kawo karshen yarjejeniyar budewa Israela wuta

January 1, 2006
https://p.dw.com/p/BvED

Hamas/Truce

Kungiyar yan gwagwarmayar palasdinawa ta Hamas tace ta kawo karshen yarjejeniyar data kulla da shugaban palasdinawa Mahmud Abbas ta dakatar da kaiwa Israela hare hare.

Kafin sanarwar tata dama wasu kungiyoyin Palasdinawan na Shahidan Al-Aqsa da ta Islamic Jihad da kuma ta popular Resistsnce dukkanninsu sun bayyana irin wannan sanarwa kuma suka ce suke da alhakin jerin hare haren makaman da ake harbawa kudancin Israela.

Kungiyar Hamas din ta kuma sha alwashin daukar fansar kisan da sojan Israela suka yiwa wasu palasdinawa biyu a arewacin zirin Gaza saoi kalilan bayan kawo karshen dakatar da bude wutar.

Hamas din tayi gargadin cewa Israela zata dandana kudarta sakamakon a yanzu da waadin yarjejeniyar ya kare, saboda ta rinka keta yarjejeniyar, ta na kaiwa palasdinawa hare hare a lokacin duk kuwa da cewa ita Hamas din ta kiyaye da yarjejeniyar da kyau.

A halin da ake ciki kuma wasu yan bindigar palasdinawa sun sace wani dan kasar Italia mai rajin tabbatar da zaman lafiya a wajen garin khan yunis kwanaki biyu kacal bayanda aka sako yan Birtaniyan nan uku da aka yi garkuwa da su.

Sai dai kuma wasu rahotanni sunce mutane biyune yan kasashen wajen da aka sace.

Wani bangare na kungiyar shahidan Al Aqsa yace shine ya sace mutumin.Sunce sharadinsu na sakin mutumin shine suna bukatar da a gudanar da cikakken bincike akan sanadin rasuwar tsohon shugaban Palasdinawa Yasser Arafat tare kuma da fitar da gurbatattun shugabannin jamiyyar Fatah mai mulkin palasdinawa .

Sakamakon tabarbarewar yanayin tsaro a yankin na palasdinawa yanzu dai ana cigaba da kiran da a dage zaben da za ayi ranar ashirin da biyar ga watannan.

Kiran na ba baynan ya fitone da ga ministan yari na palasdinu Sufiyan Abu Zaydeh.