1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hamas ta janye daga shirin dakatar da yaki da Isra´ila

June 10, 2006
https://p.dw.com/p/Buua

Kungiyar Hamas mai jan ragamar mulkin gwamnatin Falasdinawa ta harba rokoki harhadawar gida akan Isra´ila sa´o´i kalilan bayan da ta janye daga yarjejeniyar tsagaita bude wuta da Isra´ila. Hamas ta dauki wannan mataki ne don nuna fushinta game da mutuwar fararen hular Falasdinawa su 7 a wani harin makamin atileri da jiragen ruwa yakin Isra´ila suka kai jiya a Gaza. Sanarwar da Hamas ta bayar ta dakatar da yarjejeniyar tsagaita wutar ta tayar da fargabar shiga wani mummunan yanayi na kai hare haren kunar bakin wake tare da zubar da jini. Isra´ila dai ta nuna nadama game da aukuwar wannan abin da ta kira kuskure. Kakakin ma´aikatar harkokin wajen Isra´ila Mark Regev cewa yayi:

“Al´umar Falasdinu ba abokan gabar mu ba ne. Muna iya kokarin mu don kauracewa yiwa fararen hula wadanda ba su san hawa ba, ba su san sauka ba lahani. Manufar mu ita ce mu hana ´yan ta´adda kai hare haren rokoki akan unguwannin fararen hula na Isra´ila.”