Hamas ta ce Isra´ila ta ƙaddamar da yaki a kan ta | Labarai | DW | 26.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hamas ta ce Isra´ila ta ƙaddamar da yaki a kan ta

An halaka mutane biyar sannan wasu dama sun samu raunuka a jerin hare hare ta sama da Isra´ila ta kai a Zirin Gaza. Isra´ila ta kai hare haren ne akan wasu gine gine guda 4 wadanda ma´aikatar cikin gidan Falasdinawa dake karkashin ikon kungiyar Hamas ke amfani da su. Wadannan hare haren sun gurgunta kokarin da shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas ke yi na ganin an tsagaita wuta. A halin da ake ciki kungiyar Hamas ta bayyana farmakin da jiragen saman yakin Isra´ila ke kaiwa a Gaza babu kakkautawa da cewa kadamar da yaki ne akan ta. Shi kuma a nasa bangaren mukaddashin ministan tsaron Isra´ila Ephraim Sneh ya kare matakan da sojin bani Yahudun ke dauka a Zirin na Gaza.